KAFIN GIDA A GARGAJIYAR HAUSAWA
KAFIN GIDA A GARGAJIYAR HAUSAWA
No Thumbnail Available
Date
2013
Authors
RABIU, MUHAMMAD TAHIR
Journal Title
Journal ISSN
Volume Title
Publisher
Abstract
Kafi ko kuma tsarin gida ga al'ummar Hausawa, abu ne da aka
gada tun asali, wanda sukan hi wasu hanyoyi domin samar wa
kawunansu tsaro ta hanyar kafi da kuma riga-kafi a muhallansu, da
wuraren sana 'o 'insu da iyali da sauransu. Wasu Hausawa sukan yi
amfani da iskoki ko layu ko rataye da binne-binncn wasu abubuwa,
domin tsarin gida ko gari ko gona ko iyali ko wani abu mai amfani
. Ana aiwatar da haka ne domin kare mutuncin gida ta fuskar tsaro
da wanin haka. Saboda haka mukalar za ta gudanar da bayani kan
yadda kafiyake a gargajiyar Hausawa, da kuma hanyoyin da aka bi
wajen aiwatar da shi. Wadannan hanyoyi kuwa sun hada da iskoki
da hatimai,sukan yi hakan ne bisa wasu dalilai da kuma manufofi
daban-daban, wadanda suka hada da tsaro ko kuma tsaren gida ko
wajen sana'a da iyali da sauransu.
Description
Keywords
KAFIN GIDA,, GARGAJIYAR,, HAUSAWA.