TAKAICIN MATA A FINA-FINAN HAUSA

dc.contributor.authorHASSAN, BINTA
dc.contributor.authorMUSA
dc.date.accessioned2015-10-08T08:37:13Z
dc.date.available2015-10-08T08:37:13Z
dc.date.issued2009-03
dc.descriptionSASHEN HARSUNAN AFIRKA DA AL’ADU JAMI’AR AHMADU BELLO, ZARIYA.en_US
dc.description.abstractTun zamani mai tsawon gaske, an sami mata da suka yi rubuce-rubuce, suka bayyana yadda matsayin mace yake tun a wancan lokaci. Ire-iren waxannan mata sun dubi matsayin mace ta fuskar al’ada da addini da siyasa da ilimi da tattalin arziki da zamantakewa da sauransu vangarorin rayuwa, inda bayanansu suka fito da cewa duk a waxannan vangarori na rayuwa mace ta kasance qasqantacciya kuma rarrauna, har wasu ma ke xaukar ta ba ‘yar’Adam ba ce. Ganin wannan bincike ya faxo cikin wannan fage na irin takaicin da mata ke fama da shi a rayuwa ya sa aka shiga cikin duniyar nazari domin xora binciken bisa An gina wannan binciken a ka ntu rrbaa’irn d am taat adnatcaek.a da niyyar fito da abubuwan da ke sa mata shiga halin quncin rayuwa da xauki fina-finan Hausa a matsayin madubi da suka hasko waxannan abubuwa. An yi haka ne saboda an hangi wani givi da ke akwai a bincike-bincike da nazarce-nazarcen ayyukan da suka shafi mata da fina-finan Hausa. Mafi yawan manazarta sun fi bai wa ayyukan da maza da sauran sassan adabi muhimmanci, duk kuwa da cewa su akwai abin da ya kamata a binciko a kansu. Sannan su ma fina-finai matsayinsu na wani vangare na adabin Hausa xauke suke da abin da rayuwar al’umma musamman mata. Domin daidaita binciken an dubi yadda addinai da al’adu daban-dabam ke kallon matsayin mata a zamanin jahiliyya har zuwa wannan qarni. Haka kuma an kawo matsayin mata da irin gudummawar da suke bayarwa a vangaren shirya fina-finan Hausa. Domin fito da fasalin binciken fili an kawo bayanai game da samuwar fina-finan Hausa. Sannan aka kawo bayanai dangane da kalmar takaici da nau’o’insa. Haka kuma an kawo abubuwan da ke jefa mata cikin takaici da suka haxa da zamantakewa tsakanin miji da mata da kishi tsakanin kishiyoyi da kishi tsakanin faccaloli (kishiyoyin sauri) da kuma tsakanin da suruka da sarakuwa, sai kuma rashin haihuwa da haihuwar ‘ya’ya mata . Sannan kuma an kawo yadda fina-finan Hausa suka nuna yadda yara mata kan shiga qunci da takaici a sauran al’amuran rayuwa, kamar a sanadiyyar auren dole da irin yadda matar uba ke quntata wa ‘ya’yan miji, da kwaxayi da son abin duniya da kuma yadda maza kan yaudari matan su saka su cikin takaici.en_US
dc.identifier.urihttp://hdl.handle.net/123456789/6917
dc.language.isoenen_US
dc.subjectTAKAICINen_US
dc.subjectMATAen_US
dc.subjectFINA-FINANen_US
dc.subjectHAUSAen_US
dc.titleTAKAICIN MATA A FINA-FINAN HAUSAen_US
dc.typeThesisen_US
Files
Original bundle
Now showing 1 - 1 of 1
No Thumbnail Available
Name:
TAKAICIN MATA A FINA-FINAN HAUSA.pdf
Size:
2.68 MB
Format:
Adobe Portable Document Format
Description:
License bundle
Now showing 1 - 1 of 1
No Thumbnail Available
Name:
license.txt
Size:
1.58 KB
Format:
Item-specific license agreed upon to submission
Description:
Collections