TAKAICIN MATA A FINA-FINAN HAUSA
TAKAICIN MATA A FINA-FINAN HAUSA
No Thumbnail Available
Date
2009-03
Authors
HASSAN, BINTA
MUSA
Journal Title
Journal ISSN
Volume Title
Publisher
Abstract
Tun zamani mai tsawon gaske, an sami mata da suka yi
rubuce-rubuce, suka bayyana yadda matsayin mace yake tun a
wancan lokaci. Ire-iren waxannan mata sun dubi matsayin mace ta
fuskar al’ada da addini da siyasa da ilimi da tattalin arziki da
zamantakewa da sauransu vangarorin rayuwa, inda bayanansu suka
fito da cewa duk a waxannan vangarori na rayuwa mace ta kasance
qasqantacciya kuma rarrauna, har wasu ma ke xaukar ta ba
‘yar’Adam ba ce. Ganin wannan bincike ya faxo cikin wannan fage na
irin takaicin da mata ke fama da shi a rayuwa ya sa aka shiga cikin
duniyar nazari domin xora binciken bisa An gina wannan binciken a ka ntu rrbaa’irn d am taat adnatcaek.a da niyyar
fito da abubuwan da ke sa mata shiga halin quncin rayuwa da
xauki fina-finan Hausa a matsayin madubi da suka hasko waxannan
abubuwa. An yi haka ne saboda an hangi wani givi da ke akwai a
bincike-bincike da nazarce-nazarcen ayyukan da suka shafi mata da
fina-finan Hausa. Mafi yawan manazarta sun fi bai wa ayyukan da
maza da sauran sassan adabi muhimmanci, duk kuwa da cewa su
akwai abin da ya kamata a binciko a kansu. Sannan su ma fina-finai matsayinsu na wani vangare na adabin Hausa xauke suke da abin da
rayuwar al’umma musamman mata.
Domin daidaita binciken an dubi yadda addinai da al’adu
daban-dabam ke kallon matsayin mata a zamanin jahiliyya har zuwa
wannan qarni. Haka kuma an kawo matsayin mata da irin
gudummawar da suke bayarwa a vangaren shirya fina-finan Hausa.
Domin fito da fasalin binciken fili an kawo bayanai game da
samuwar fina-finan Hausa. Sannan aka kawo bayanai dangane da
kalmar takaici da nau’o’insa. Haka kuma an kawo abubuwan da ke
jefa mata cikin takaici da suka haxa da zamantakewa tsakanin miji da
mata da kishi tsakanin kishiyoyi da kishi tsakanin faccaloli (kishiyoyin
sauri) da kuma tsakanin da suruka da sarakuwa, sai kuma rashin
haihuwa da haihuwar ‘ya’ya mata . Sannan kuma an kawo yadda
fina-finan Hausa suka nuna yadda yara mata kan shiga qunci da
takaici a sauran al’amuran rayuwa, kamar a sanadiyyar auren dole da
irin yadda matar uba ke quntata wa ‘ya’yan miji, da kwaxayi da son
abin duniya da kuma yadda maza kan yaudari matan su saka su cikin
takaici.
Description
SASHEN HARSUNAN AFIRKA DA AL’ADU
JAMI’AR AHMADU BELLO, ZARIYA.
Keywords
TAKAICIN, MATA, FINA-FINAN, HAUSA