KWATANCIN BORIN HAUSAWA DA NA GBAGYI

dc.contributor.authorHALIRU, MUSA KUTA
dc.date.accessioned2015-01-27T11:51:13Z
dc.date.available2015-01-27T11:51:13Z
dc.date.issued2014-04
dc.descriptionA thesis submitted to the School of Postgraduate Studies, Ahmadu Bello University, Zaria - Nigeria In partial fulfilment of the requirements for the Award of Degree of Master of Arts in African Languages and Cultures (Hausa). Department of African Languages and Cultures, Faculty of Arts Ahmadu Bello University, Zaria-Nigeria. APRIL, 2014en_US
dc.description.abstractWannan bincike ya kwatanta borin Hausa da na Gbagyi (Gwari) domin nuna kamanci da bambanci da ke tsakaninsu. Samuwar Iskoki dai wani imani ne da kowace al’adar al’ummar duniya ta yi imani da shi. Imanin mutanen duniya game da Iskoki abu ]aya ne ta fuskar kasancewarsu ~oyayyu, buwayayyu, masu ban tsoro, masu karkatar da mutane, kuma masu }arfi a kan mutane. Shi kuma bori a matsayin bautar Iska da]a]]iyar al’ada ce, da ke cikin hanyoyin addinin gargajiya na Hausa da kuma Gbagyi. Don haka, ha]uwa da zamantakewa da Hausawa suka yi da Gbagyi ya haddasa sauye-sauye na yanayin aiwatar da borin Gbagyi ta fuskokin sunayen Iskoki ko Aljannu da halayen ‘yan bori da tufafin ‘yan bori da kayan ki]an ‘yan bori da girka da kuma amfanin ‘yan bori ga jama’a. Wannan bincike ya fito da wa]annan sauye-sauye a fili domin a fahimci kamanci da kuma bambancin borin al’ummun guda biyu. Daga cikin batutuwan da aka tattauna akwai tarihin Hausawa da Gbagyi, da borin Gbagyi na asali kafin su ha]u da Hausawa. A farkon wannan bincike, an kawo borin Hausawa, sannan an nuna dangantakar Hausawa da Gbagyi ta yadda suka ha]u har borinsu ya haddasa sauyi a kan na juna musamman a manyan garuruwan Gbagyi da aka yi bayanin ha]uwarsu kamar: Kuta da Minna da Suleja duk na jihar Neja da kuma Birnin Gwari ta jihar Kaduna. A }arshe, binciken ya gano matsanancin tasirin da borin Hausawa ya yi a kan na Gbagyi ta yadda a yau, kusan dukkan ‘yan borin Gbagyi, suna aiwatar da bori ne ta salon yadda suka ga ‘yan borin Hausawa na aiwatarwa.en_US
dc.identifier.urihttp://hdl.handle.net/123456789/5941
dc.language.isoenen_US
dc.subjectKWATANCIN,en_US
dc.subjectBORIN,en_US
dc.subjectHAUSAWA,en_US
dc.subjectGBAGYIen_US
dc.titleKWATANCIN BORIN HAUSAWA DA NA GBAGYIen_US
dc.typeThesisen_US
Files
Original bundle
Now showing 1 - 1 of 1
No Thumbnail Available
Name:
KWATANCIN BORIN HAUSAWA DA NA GBAGYI.pdf
Size:
3.15 MB
Format:
Adobe Portable Document Format
Description:
License bundle
Now showing 1 - 1 of 1
No Thumbnail Available
Name:
license.txt
Size:
1.58 KB
Format:
Item-specific license agreed upon to submission
Description:
Collections