KWATANCIN HABARCEN NIJERIYA DA NIJER : TSOKACI A KAN TATSUNIYA
KWATANCIN HABARCEN NIJERIYA DA NIJER : TSOKACI A KAN TATSUNIYA
No Thumbnail Available
Date
2018-05
Authors
TAHIR, Muhammad Rabiu
Journal Title
Journal ISSN
Volume Title
Publisher
Abstract
Habarcen tatsuniya a matsayin hanyar nazari, wacce aka yi amfani da ita wajen kwankwance tatsuniyoyin al‟ummomin da ita. Al‟ummar Hausawa suna da nau‟o‟in habarcen tatsuniyoyi da dama, wa]anda suka ha]a da labari da tarihih da hikaya da almara da sauransu. Nazarin ya yi amfani da ra‟in kwatantan adabi wanda ake amfani da shi wajen kwatanta adabin al‟ummomi wa]anda ake ganin suna da wata dangantaka ko kuma wasu kamanni a wasu ~angarori na adabi ko al‟adu domin a tabbatar da ala}arsu. An kwatanta tatsuniyoyin al‟ummomin Hausa a ~angaren arewacin Nijeriya da kuma Jumhuriyar Nijer. Bincike ya kwatanta yanayin tatsuniyoyin da jigo da salo da kuma adon harshen ta hanya kwatanci. Nazarin ya gano abubuwa masu kama da juna da kuma wa]anda suka bambanta da juna a duka tatsuniyoyin al‟ummomin biyu. Misali idan aka yi la‟akari da jigo a tsarin sarautar gargajiya, musamman dangantakar sarki da talaka sun bambanta. Haka kuma a ~angaren taurari al‟ummomin suna da ala}a da juna ta fuskar tauraro gizo da matarsa }o}i, da kuma ala]ar sarkin agadas da ]ansa yarima, ana iya fahimtar haka a ta fuskar raurari kamar gizo da sauransu. Har ila yau, a zubin labari kuma a inda aka rasa sulmoyiwar labara a habarcen tatsuniyar Jumhuriyar Nijer. Wannan bambanci da kuma kamanni ya faru ne kamar yadda binciken ya gano suna da ala}a da muhalli da tattalin arziki da zamantakewa da kuma tasirin Turawan mulkin mallaka.
Description
BINCIKE DOMIN NEMAN DIGIRIN {OLI (Ph.D)
A SASHEN HARSUNA DA AL‟ADUN AFIRKA
TSANGAYAR FASAHA
JAMI‟AR AHMADU BELLO,
ZARIYA-NIJERIYA
Keywords
KWATANCIN HABARCEN NIJERIYA,, NIJER,, TSOKACI,, TATSUNIYA,